A wannan sashe mun tanadar muku sautuka da wakoki masu citta domin jin dadi da nishadin ku. 

Akwai wakoki daga manya da kuma gogaggun fasihai, wadanda zaku iya sauraro kuma ku iya sauke wasu daga ciki kyauta. Wadannan wakoki sun kasance karkashin salon wakoki na Gamza da kuma Taushi (Rap & R&B) a harsunan Hausa da na Turanci. Tukuicin da zaku iya ba wadannan jajirtattun fasihai da suka baku damar nishadantuwa da guminsu kyauta itace, ku taya su kishi ta hanyar yada wadannan wakoki ga sauran ‘yan uwa da abokan arziki, abunda kawai suke bukata kenan.

Bayan wakokin sauraro, akwai tsirarun wakoki da muka samu izinin dora muku su a nan domin jin dadin kallon ku, sannan muna muku alkawarin zamu dora muku wasu sabbi yayin da muka samu izinin dora su.

Akwai sautukan sauraro harlau, wadanda suka kunshi labaran ban dariya da nishadi, akwai na tausasa zuciya domin ‘yan soyayya, hakazalika akwai na nusar da mai sauraro akan muhimman darussan rayuwa da hikimomin gudanar da ita.

Daga nan kuma akwai cikakkun sautukan shirin rediyo da “Mai Suburbuda” ke gabatarwa a tashar Dala FM dake jihar Kano. Zaku iya sauraro da saukewa domin sauraro daga baya ko turawa ga na kusa.

 

Wakokin Sauraro
Wakokin Kallo
Sautukan Nishadi da karfafa gwiwa
Shirin Rediyo
search previous next tag category expand menu location phone mail time cart zoom edit close