MARABA!

A madadin dukkan daukacin ma’aikatan wannan kamfani, ni shugaban wannan kamfani ina muku maraba izuwa sansanin mu na yanar gizo. Bazan iya misalta farin cikin da nake ciki ba a halin yanzu kasancewar yau gashi an wayi gari a dalilin goyon baya da kauna da kuke nuna mana, gashi yau mun samu jaririn kamfaninmu ya zama saurayi.
A tafiyar da muka shafe shakaru kusan goma muna yi (daga 2009-2018), zan iya cewa mun samu nasarori dayawa a fannoni daban-daban, wadanda suka kasance kamar haka –

"Sadiq Salihu Abubakar" inkiya "Buzo Danfillo" inkiya "Mai Suburbuda". Makirkiri kuma Shugaban Kamfanin Algaita Dub-Studio.

Jaddada amfani da harshen hausaKasancewar muna fassara fina-finan yarurruka daban-daban izuwa hausa, hakan ya samar da nasarar jaddada amfani da harshen hausa domin madadin kallon fina-finai a yaren da ba na hausa ba, sanadiyyar fassara miliyoyin mutane hatta wadanda ba hausawa ba suna kallo, hakazalika suna amfani da kalamai shudaddu, hakazalika da ma kirkirarru na hausa wajan magana ko isar da sako.

Samar da sabbin kalamai. Yayin gudanar da ayyukan fassara mun samu kanmu muna cin karo da wasu kalamai wadanda babu tanadin su a harshen hausa, mu kuma daga cikin tsarinmu tunda mun ce fassara mukeyi, to lallai mun damu da tabbatar da cewa duk wata kalma da zamuyi amfani da ita, lallai ilalla bukatarmu wannan kalma ta zama ta hausa.  Hakan ya sa muka fara samar da kalamai a cikin tafiyar ayyukanmu, wanda hakan yunkuri ne na samar wa da harshen Hausa ‘yancin dogaro da kai, hakazalika fadada huruminsa wajan isar da katafaren jerin sakonni a iya farfajiyar nahawunsa ba tare da ketare katangar sa ba.

Wayar da kan al’umma. Duk da cewa dukkannin fina-finan da ake fassarawa, an shirya su ne a yankunan gabashi da yammacin duniya, wanda ke nufin ba lallai bane tsarin rayuwa, ra’ayoyi, alkiblu da sauran nau’o’in dabi’u na can su kasance iri daya da na yankunan afurka, ko na Hausawa ba, ya zamana akwai abubuwa dayawa da suka shafi zamantakewa, matsalolin rayuwar talaka, zaluncin shuwagabanni, larurorin matasa misali shaye-shaye, dabanci da sauransu musamman a fina-finan yankin indiya, da sukayi kamanceceniya da irin na yankunan kasashen afurka har ma da na Hausa, lamarin da ya taimaka wajan wayar wa da masu kallo kai, dangane da yadda ake bullowa wasu matsaloli, hakazalika da yadda doka take sarrafuwa wajan samar da adalci ga wanda aka zalunta, har ma da nunar da darussa masu koyar da jajircewa, yarda da kai da kuma kasancewa da kwarin gwiwa a mawuyacin hali, banda ilimomi da suka danganci fasahar zamani da kuma yadda ake sarrafa su wajan samar da sauki da cigaba a rayuwar al’umma.

Gabatar da nishadi ga al’umma. Rayuwar dan adam bata kammaluwa idan babu nishadi da annashuwa, domin kunci da nauyin zuciya sune kan haifar da munanan sakamako ga lafiya da kuma walwalar dan adam. Harkar fassara ta samar da faffadar farfajiya mai cike da nau’o’in nishadi daban-daban kama daga barkwanci, caskale, sarrafa kalamai, hikimomin rayuwa, izuwa nuni ga muhimmancin abubuwa masu muhimmanci, da dai sauransu duk cikin salsala ta nishadantarwa, raha, ban al’ajabi, ban tausayi da kuma shauki.

Kirkiro sabuwar kasuwa. Matasa dayawa a sanadiyyar harkar fassara fina-finai izuwa harshen Hausa, sun samu madogarar sana’a domin kuwa kama daga kasuwanci, dillanci, siyar da daidaya (cinda), tsara hoton jikin madaukar faifan kallo (tsahoton faika), buga hoton madaukar faifan kallo (buhoton faika) izuwa safarar faya-fayen zuwa kasashen ketare irinsu Nijar, Ghana, Kamaru da dai sauransu, wannan aiki na fassara ya zamo silar rufin asiri ga mutane dayawa.

search previous next tag category expand menu location phone mail time cart zoom edit close